Amurka ta bukaci jami’anta da su fice daga Abuja

0
43

Kasar Amurka ta bukaci jami’an diflomasiyar ta dake aiki a birnin Abujan Najeriya da su fice daga garin domin kaucewa hare haren ta’addancin da tace akwai yiwuwar kaiwa.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta gabatar da wannan sanarwa wadda ta bukaci ficewar jami’an diflomasiyyar da ayyukansu basu zama wajibi ba da su fice tare da iyalansu saboda karfin barazanar da suka ce birnin ke fuskanta.

Ita dai wannan sanarwar bata bayyana shirin kwashe jami’an diflomasiyar ba, amma tayi gargadi ga Amurkawa akan kaucewa tafiye tafiyen da basu zama wajibi ba zuwa Najeriyar kanta, saboda damuwar da take da ita akan aikata laifuffuka da kuma rashin kwanciyar hankali.

Wannan gargadin na zuwa ne kwana biyu bayan wadda ta gabatar a karshen mako wanda yake cewa akwai yiwuwar kai harin ta’addanci a birnin Abuja, kuma tuni wasu kasashen yammacin duniya irin su Birtaniya da Canada da kuma Australia suka gabatar da irinsa.

Kasar Amurka bata yi cikkaken bayani akan irin barazanar birnin na Abuja dake dauke da mutane sama da miliyan 6 ke fuskanta ba, sai dai masana harkar tsaro na danganta wannan gargadi da karuwar hare haren ‘yan ta’adda a Najeriya musamman ganin yadda suka fasa gidan yarin Kuje suka kuma fitar da wasu abokan aikin su a watannin da suka gabata.

Sai dai hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta bukaci jama’ar kasar da su kwantar da hankalinsu, inda tace tana aiki tare da wasu hukumomin tsaro domin kare lafiyar jama’ar birnin da kuma kasa baki daya.