Mutane 120 ne suka mutu 150 kuma suka jikkata sakamakon turmutsitsi a birnin Seoul

0
90

Hukumomin kasar Koriya ta Kudu sun tabbatar da mutuwar mutane 120, yayin da wasu sama da 150 suka samu raunuka sakamakon tirmitsitsin da aka samu lokacin bikin ‘halloween’ da mutane suka yi dandazo a Birnin Seoul.

Wani jami’in hukumar kasha gobara a kasar, Choi Sung-bum yace ya zuwa karfe 1.30 na agogon ranar kasar yau, an tabbatar da mutuwar mutanen 59, yayin da sama da 150 suka samu raunuka, wasu daga cikin su kuma raunin su yayi tsanani.

Kamfanin dillancin labaran kasar na Yonhap ya bayyana cerwar jami’an agaji na ci gaba da kwashe gawarwakin mutanen da suka mutu a jakankuna dibar gawarwaki, yayin da jami’an lafiya ke kula da wadanda suka samu raunuka.

Babu wani bayani akan abinda ya haifar da wannan hadari, amma shugaban kasar Yoon Suk-yeol ya kira wani taron gaggawa domin tattauna iftila’in da aka samu.

Rahotanni sun ce akalla mutane sama da dubu 100 suka halarci gangamin wanda shine irinsa na farko da akeyi bayan annobar korona.