Lula ya lashe zaben shugaban kasa a Brazil

0
81

Tsohon shugaban kasar Brazil Luiz InĂ¡cio Lula da Silva ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, inda ya kayar da shugaba mai ci Jair Bolsonaro wanda ya so samun wa’adi na biyu.

Lula ya lashe zaben da kashi 50.83 cikin 100 na dukkan kuri’un da aka kada, yayin da Bolsonaro ya sami kashi 49.17 cikin 100 na kuri’un bayan da aka kidaya kimanin kashi 99 cikin 100 na dukkan kuri’un da aka kada zuwa karfe 11 na dare.

Za a rantsar da sabon shugaban kasar ranar 1 ga watan Janairun shekara 2023.