Buhari zai tafi Landan ganin likita

0
97

Shugaba Muhammadu Buhari ya shirya sake tafiya birnin Landan domin ganin Likita.

Buhari zai kama hanyarsa ta zuwa birnin Landan a yau Litinin kamar yadda Fadar Gwamnatin Najeriya ta tabbatar.

Kakakin shugaban, Femi Adesina a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce ana saran Buhari zai dawo gida a cikin mako na biyu na watan Nuwamba.

Ba wannan ne farau ba domin kuwa Buhari ya sha tafiya Landan domin duba lafiyarsa tun lokacin da ya fara jagorantar kasar.

A 2017, Buhari ya kwashe kwanaki 150 a Birtaniya a wata tafiyar duba lafiyar da ba a bayyana abin da ke damun shi ba.

Buhari ya kara komawa Birtaniya a watan Mayun 2018 domin ganin liktansa, inda ya yi kwana hudu kacal a kasar.

A watan Nuwambar 2020 ne, mai dakin Shugaban Kasar, Aisha Buhari, ta ce akwai bukatar inganta bangaren lafiya a Najeriya domin a rage tafiye-tafiyen neman magani kasashen waje.