Buhari ya jajantawa Koriya ta kudu kan rasuwar mutane 151 yayin turmutsutsi

0
103

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa shugaba Yoon Suk-yeo, gwamnati da al’ummar Koriya ta Kudu bisa turmutsutsin da aka yi a ranar Asabar a gundumar Itaewon da ke birnin Seoul inda matasa da dama suka rasa rayukansu.

Akalla mutane 151 ne aka rahoto sun mutu, wasu 82 kuma suka samu raunuka yayin turmutsutsin da ya barke a gundumar yayin da suke bikin Halloween.

Turmutsitsin na bikin Halloween, ya rutsa da matasa da dama yayin da matasan suka bi ta cikin wata kuntattar hanya.An kiyasta cewa kusan mutane 100,000, galibinsu matasa ne da kuma wadanda suka kai shekaru ashirin ne suka halarci bikin Halloween din a daren ranar Asabar, inda suka toshe lunguna da sako na yankin.

A sakon ta’aziyyarsa ga takwaransa na Koriya ta Kudu, Buhari ya aika da addu’o’in fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.