Dalilan da suka sanya Rasha ta zafafa hare-hare a Ukraine

0
91

Sabbin hare-haren da aka kai a Ukraine na zuwa ne bayan da Rasha ta dora alhakin harin da wani jirgin sama mara matuki ya kai kan jiragen a tekun Black Sea a yankin Crimea.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, a ranar Asabar din da ta gabata ne, aka lalata wani jirgin ruwan yaki na kasar Rasha a birnin Sevastopol mai tashar jiragen ruwa a wani harin da aka kai da kuramen jiragen yaki.

Har ila yau, Rasha ta zargi wasu kwararrun Birtaniya da horar da sojojin Ukraine wadanda suka kai hare-hare a yankin Crimea, da ke kudancin Ukraine, da Rasha ta mamaye a shekarar 2014.

Ukraine dai ba ta ce uffan ba game da wannan batu, yayin da ma’aikatar tsaron Burtaniya ta ce Rasha na shirya labarun kanzon kerege ne, domin zafafa hare hare a kasar.

Har ila yau, Rasha ta sanar da janyewa daga yarjejeniyar da kasashen duniya suka kulla wadda ta bai wa Ukraine damar fitar da hatsi daga tashoshin jiragen ruwan tekun Black Sea.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce jiragen da aka yi amfani da su a harin na ranar Asabar sun kaddamarwa jiragen ruwa da ke da hannu a yarjejeniyar cinikin hatsi.

Hukumomi a Ukraine sun ce Rasha ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami a fadin kasar, ciki har da babban birnin kasar Kyiv, lamarin da ya janyo katsewar wutar lantarki da kuma ruwan sha.

An kuma bayar da rahoton harin makami mai linzami a yankin tsakiyar Vinnytsia, da Dnipropetrovsk da Zaporizhzhia a kudu maso gabas, da Lviv a yammacin Ukraine.

Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa an kai hari a cibiyar samar da wutar lantarki ta Dnipro dake yankin Zaporizhzhia.