An shawarci mazauna birnin Abuja su sanya kyamarorin tsaro a gidajensu

0
136

Hukumomin Abuja babban birnin Najeriya sun shawarci mazauna birnin da su saka kyamarorin tsaro a gidajensu domin sama wa gwamnati saukin magance matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.

A wata sanarwa da babban daraktan hukumar fasaha da sadarwa na birnin Muhammad Sule ya fitar, ya ce hukumomin birnin sun bayar da shawarar ne a yayin zaman majalisar zartarwar birnin da aka gudanar a gundumar Gwarimpa.

Taron – karkashin jagorancin babban sakataren birnin tarayya Mr Olusade Adesola, wanda ya wakilci ministan tarayya Malam Muhammad Bello – ya samu halartar manyan sakatarorin hukumomin birnin daban-daban.