Kamfanin shafin sada zumunta na Instagram ya rufe shafin dan Najeriyar nan dan kwalisa wanda aka kama da laifin zamba a kasashen duniya, Hushpuppi, saboda ya saba dokokinsu na zamba.
A wata sanarwa da kamfanin Meta wanda shi ne kuma mai Facebook da WhatsApp ya fitar, ya ce, “Ba ma son wani mutum ya yi amfani da manhajojinmu ya yi zamba ko ya ci da gumin mutane.
“Kuma muna da dokoki karara a kan zamba – hadi da sauya kudaden haram.”
Sanarwar kamar yadda ta shaida wa BBC ta yi bayani da cewa, “Mun rufe shafin@hushpuppi saboda saba wadannan dokokin.”
Hushpuppi, wanda ainihin sunansa shi ne Ramon Abbas, yana sanya hotuna na kwalisa da dukiya da abubuwa na attajirai a shafinsa na Instagram.
A irin wallafe-wallafe da matashin mai tarin mabiya yake yi, yana nuna irin rayuwar da yake yi ta bushasha ga mabiyansa miliyan 2.8.
To amma kwatsam sai ruwa ya kare wa dan kada inda aka damke shi a Dubai inda yake zaune a watan Yuni na 2020.
Kasa da shekara daya bayan kama shi sai ya amsa laifin da aka zarge shi da shi na sauya kudin haram a wata kotu a Amurka.
Kazalika, an dauke shi a matsayin daya daga cikinta kasurguman mazambata na duniya, kamar yadda Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI ta ce.
Bayanai sun nuna cewa a laifukansa ya yi zambar kusan dala miliyan 24, kuma a yanzu yana fuskantar hukuncin daurin shekara 20 a gidan yari.
Duk da amsa laifinsa, kamfanin Instagram bai rufe shafin nasa ba a shekarar da ta wuce, a lokacin da cewa sun gudanar da bincike kuma suka ga babu dalilin da zai sa su rufe.