Ban yi fada da dan takarar mataimakin gwamnan Kano ba – Doguwa

0
126

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya karyata cewar shi da dan takarar mataimakin gwamnan a jam’iyyar APC a Jihar Kano Murtala Sule Garo sun bai wa hammata iska a wani taron masu ruwa da tsaki na APC a gidan dan takarar gwamna na jam’iyyar, Nasiru Yusuf Gawuna.

Doguwa, a wata hirarsa da manema labarai ya ce, “Ina matukar girmama Sule Garo, mu ma ako da yaushe, Ina mai fatan in ga ya zama matatakin gwamna shi da kuma Gawuna a matsayin zababben gwamnan Kano.

“A rubuce yake, babu inda na taba nuna wa Sule rashin girmamawa ko kuma na yin furucin banza a kan shi, amma sai dai, shi ya jima yana son ya ga faduwata, ba sau daya ba sau biyu ba, kamar yadda ya nuna a yayin da dan takarar shugaban kasa Ahmad Bola Tinubu ya zo Kano”.

A cewarsa, “abin da ya faru shi ne, an kira gwamna an ce min shugaban jam’iyyarmu na son gani na, inda ya dace in same a gidan Gawuna, inda suke yin ganawar, na wuce kai tsaye zuwa dakin da suke yin gawanar na yi magana da shugaban jam’iyyar.

“Kamar yadda da dai Sule Garo ya saba yin kalamansa na zargi, sai ya umarce ni da in fice daga dakin, inda ya kara da cewa, duk da na shaida wa Sule Garo, na zo in ga shugaban jam’iyya ne, sai ya ci gaba da zagina, inda hakan ya fusata ni na mayar da nawa martanin.

”Doguwa ya yi ikirarin cewa, Sule Garo ya yi yunkurin kai masa suka, amma ya zame ya fada a kan tebur da aka dora kofunan tangaran na shan shayi, inda da hakan ya janyo ya ji wa kansa rauni.