Mun dana wa wasu gwamnoni 3 tarko kan wasu makudan kudade – EFCC

0
98

Gwamnonin Jihohi uku da ke kan karagar mulki sun shiga komar EFCC kan yunkurin karkatar da kudade ta hanyar biyan albashin ma’aikatan jihohinsu.

Shugaban Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati, Abdulrasheed Bawa, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.

Bawa, wanda bai bayyana sunayen gwamnonin ba, ya ce biyu daga cikinsu ‘yan Arewa ne, yayin da na ukun ya fito ne daga kudancin kasar nan.

Ya ce bayanan da hukumar ta samu sun nuna cewa gwamnonin uku sun kammala shirye-shiryen shigar da kudaden a cikin tsarin biyan albashin ma’aikatan jiharsu.

“Bari na fada muku wani abu; bayanin da nake da shi jiya kuma zan so ku dauki wannan abu da muhimmanci. Tuni dai wasu gwamnonin jihohin suna da wasu makudan kudaden da aka boye a gidaje daban-daban, sauran kuma suna kokarin biyan kudin cikin tsarin albashi a jiharsu,”

kamar yadda ya shaida wa Daily Trust.

Da aka yi masa tambayoyi kan ko hukumar za ta gayyaci gwamnonin, Bawa ya ce suna sa ido sosai a kan su.

“Ban san yadda suke son cimma hakan ba amma dole ne mu hana su yin hakan. Muna aiki, har yanzu ba su biya albashin da tsabar kudi ba amma abu ne mai matukar mamaki,” in ji shi, inda ya ce matakin ya sabawa sashe na 2 na dokar hana barnar kudade.

“Dokar ta fito karara game da hada-hadar kudi. Duk wanda zai ci gaba da duk wata mu’amalar kudi a matsayinsa na mutum, idan ba ta hanyar hada-hadar kudi ba, to bai kamata ya wuce miliyan 5 ba, kuma idan ya kai sama da haka ya zama laifi a gare ku.

“Eh, na yarda albashin bai kai haka ba amma me ya sa kwatsam suka koma biyan mutane albashi ta ta hannu a maimakon asusun ajiyarsu na banki?

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Babban Bankin Nijeriya ke yunkurin sake fasalin takardun kudi na N200, N500 da N1000.

A ranar 26 ga watan Oktoba ne CBN ya sanar da cewa za a sake fasalin kudin kasar nan don magance matsaloli da dama da ke da illa ga tattalin arzikin Nijeriya.