Dan takarar shugaban kasa na Jamâiyyar PDP, Atiku Abubakar, yayi alkawarin rage haraji da kuma hako danyen mai da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da Tafkin Chadi idan ya ci zabe.
Dan takarar, yayin kaddamar da yakin neman zabensa na yankin Arewa maso Gabas, a Maiduguri, Jihar Borno, ya yi alkawarin farfado da Tafkin Chadi, bukatar da ya ce, Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Garbai, ya yi.
âNa biyu shi ne mu farfado da Tafkin Chadi domin manoma su koma gonakinsu su ci gaba da samar da abinci da ayyukan yi.
âYa bukaci mu tabbata kananan hukumomi sun samu wutar lantarki, muka yi alkawarin yi.
âHaka kuma ya bukaci mu dawo da hakar danyen mai a yankin Tafkin Chadi, shi ma mun yi masa alakwarin da yardar Allah.â