An kai wa kasar Poland hari

0
124

Gwamnatin Poland ta yi kira ga al’ummarta da su kwantar da hankalinsu,  bayan  da mutum biyu suka rasa rayukansu sanadin  fadawar wani makami mai linzami a wani kauye da ke kusa da kan iyakar kasar da Ukraine.

Shugaba Andrzej Duda ya ce makami ne da aka kera a Rasha amma babu cikakken bayani a kan wanda ya harba shi.

Shugaba Duda ya fada wa ‘yan jarida cewa : ”Ba mu da wata kwakkwarar shaida ya zuwa yanzu a kan wanda ya harbo makamin, akwai yuwar cewa makami ne  da aka kera a Rasha amma wani abu ne da ake gudanar da bincike a kansa a halin yanzu.”

Firaministan Poland Mateusz Morawiecki  ya ce gwamnati za ta tsaurara tsaro a sararin samaniyar kasar  sakamakon al’amarin da ya faru.

“ Mun yanke shawarar ganin cewa wasu daga cikin zababbun rundunoninmu na dakarun kasar  sun kasance cikin shirin ko-ta-kwana musamman a fannin da ya shafi sa ido a kan  sararin samaniya” a jawabin da ya yi wa ‘yan jarida.

Al’amarin wanda ya janyo damuwa tsakanin mambobin kungiyar tsaro ta Nato wanda Poland mamba ce a ciki ya janyo musayar kalamai tsakanin Kyiv da kuma Moscow.

Rasha ta bayyana ikirarin da ake yi a kan cewa ita ce ta ke da alhaki a matsayin takalar fada daga wurin Kyiv wadda manufarta ita ce ta ja sauran kasashen duniya a cikin rikici  dan a yi mata taron-dangi

Sai dai a daya bangaren Ukraine ta yi watsi da zargin na Rasha, a kan cewa ita ce take da alhakin harin a matsayin ba komai ba ne illa kutungwila ce kawai daga Rasha.

Ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba a shafinsa na Twitter ya ce: ”A yanzu Rasha ta gabatar da wani bayani da ya yi zargin cewa makamin  tsaron sararin samaniyar Ukraine ne ya fada a yankin Poland. Wannan kuma ba dai dai ba ne.