Hukumomin kasar jamhuriyar Nijar sun ce sun fara bincike kan yadda mawakan nan biyu ‘yan Najeriya suka mallaki takardun kasar na bogi da aka kama su da su.
A yanzu haka dai ana ci gaba da tsare Mubarak Abdulkareem wanda aka fi sani da 442 da manajansa Ola Of Kano a gidan yarin birnin Yamai inda suke zaman jiran kammala bincike kamar yadda babban mai shigar da kara na gwamnati ya shaidawa manema labarai.
Babban mai shigar da kara na kasar ya ce babban laifi ne yin amfani da takardun bogi a jamhuriyar Nijar , ya kara da cewa sun bayar da umarni a gudanar da bincike domin gano hakikanin gaskiya game da lamarin.
Ya ci gaba da cewa ”Duk wanda aka samu da laifi za mu tasa keyarsa zuwa gaban kotu, ba za mu yadda wasu su rika amfani da takardun kasarmu ta hanya wadda take ba ta gaskiya ba, kuma nan gaba duk wanda aka kama da irin wannan laifin to ya kuka da kanshi”.
To sai dai kungiyoyi masu rajin kare hakkin bil adama sun fara kiraye-kirayen a bincika domin gano yadda aka yi mawakan suka samo takardun zama ‘yan kasar, kasancewar sun samo takardun ne a wasu wuraren kafin su zo wajen da za a yi musu fasfo, tare da kiran a yi musu adalci kamar yadda shugaban muryar Talaka na Jamhuriyar Nijar Alhaji Nasiru Saedu ya shaida wa BBC.
Babban mai shigar da karar ya yi watsi da rade-radin da ake yadawa cewa ana neman belinsu kan sefa (CFA) ta nijar miliyan 10, yana mai cewa har yanzu babu wata takarda da ke nuna hakan da ta zo gabansa, kuma a cewar sa idan ma ta zo, to hakan ba zai taba tabbata ba sai da amincewarsa ko akasin haka.
BBCHausa