Malaman jami’ar Yobe sun yi zanga-zanga kan rashin biyansu albashi

0
125

Mambobin Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), a Jami’ar Tarayya Gashu’wa, reshen Jihar Yobe, a ranar Talata sun gudanar da zanga-zangar lumana kan rashin biyansu albashi.

Shugaban reshen, Dakta Melemi Abatcha, ta ce zanga-zangar na nuna adawa da yadda ake musguna wa malamai ta hanyar jefa su cikin kangin yunwa.

Abatcha ta jaddada cewa, maimakon magance manyan bukatu da kungiyar ta gabatar, gwamnatin tarayya ta hanyar hukumominta, ta yi amfani da kalaman batanci da kuma tsoratarwa, inda ya kara da cewa irin wadannan zarge-zarge na cin karensu babu babbaka ta hanyar kin biyansu albashin watan Oktoba.

A yayin da ta ke kira ga gwamnatin tarayya da ta mutunta yarjejeniyar da suka kulla tare da biyan duk wani albashinsu, shugabar ASUU ta ci gaba da cewa kungiyar ta yi watsi da wulakanci da ake yi wa malaman jami’o’in Nijeriya.

An ga ‘ya’yan kungiyar dauke da alluna masu rubuce-rubuce daban-daban inda suka dinga zagaye jami’ar suna nuna rashin jin dadinsu.