Rikicin nadin sarauta ya yi ajalin dagaci a Neja

0
180

Wasu masu tayar da zaune tsaye sun kashe dagacin kauyen Lambata da ke Karamar Hukumar Gurara a Jihar Neja, Alhaji Mohammed Abdulshakur Lambata.

 Alhaji Mohammed Abdulshakur Lambata

Wakilinmu ya ruwaito cewa, an fara kai wa dagacin hari ne da safiyar ranar Asabar yayin da ya halarci wani taro amma ya tsallake rijiya da baya.

Dansa mai suna Zakari Musa, ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa maharan sun kashe mahaifin nasa ne ta hanyar sara da adduna da duka da bulalai, kuma nan take ya ce ga garinku nan.

“Har gida maharan suka biyo shi suka kashe shi.

“Da safiyar ranar Asabar suka fara kai masa harin yayin da halarci wani taro a hedikwatar Karamar Hukumar Lambata, amma ya tsallake rijiya da baya.

“Sai suka [maharan] sake biyo shi har gida da misalin karfe 1 na rana, suka kashe shi da adduna, sanduna da sauran miyagun makamai.

“Kuma duk wannan lamari ya faru ne saboda nadin sarauta da Sarkin Suleja ya yi masa shekaru uku da suka gabata.

“Masu adawa da shi na ganin su ya kamata su gaji sarautar don haka bai cancanci rawanin ba, har dai zuwa yanzu da aka yi ta fadi-tashi suka kashe shi.

AMINIYA