A bayyana yake cewa a halin yanzu Nijeriya na fadi tashi a neman samar da ci gaba a bangarori da dama, tun daga bunkasar tattalin arzki zuwa samar da ingantaciyar rayuywa ga al’umma, ana fuskantar matsaloli da dama da suke kawo wa Nijeriya cikas a kokarinta na neman ci gaba.
Amma tabbas akwai hanyoyin da suka kamata Nijeriya ta bi wajen samun mafita tare da maganin wadannan matsalolin, sun kuma hada da sanya ido da kuma karfafa mahukunta na jihohi don su tabbatar da gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon amana, hakanan a tabbatar da matakin kananan hukumomi na yin aiki yadda ya kamata, musamman ganin sune a kusa da al’umma.
Daya daga cikin manyan matsalolin da ake fuskanta a Nijeriya shi ne na rashin kyakkyawar gwamnati a matakin jihohi, jihohi da dama sun zama dandalin cin hanci da rashawa suna gudanar da ayyukansu a kudundune wanda hakan yana shafar kokarin cigaba a fadin kasar nan. In har ana son Nijeriya ta samu ci gaban da ya kamata dole a sa ido a yadda Jihohi suke gudanar da ayyukansu tare da hukunta jami’an da aka tabbatar sun aikata ba daidai ba a dukkan matakan tafiyar da harkokin jihar.
Daya daga cikin hanyoyin tabbatar da ganin haka shi ne karfarfawa jami’an gwamnatin gwiwa jihohi su gudanar da harkokin mulki a bayyane ba tare da boye-boye ba. Za kuma a iya cimma wannan manufar ta hanyar yin amfani da dokar bayyana ayyukan gwamnati a kuma ba al’umma damar sanin dukkan yadda gwamnatin ke gudanar da ayyukanta don kowa ya sani.
Haka nan za a iya cimma wannan maufan ne ta hanyar amfani da fasahar bibiyar yadda ake aiwatar da kasafin kudi, ta haka ne al’umma za su iya sani tare da bibiyar yadda ake kashe kudadensu, suna kuma iya kama duk wani jami’in gwamnatin da ya kauce hanya ko kuma ya yi halin bera.