An sare wa shugaban karamar hukumar Imo kai, sa’o’i 48 da sace shi

0
101

Kasa da sa’o’i 48 da sace shi, masu garkuwa da mutane sun fille kan shugaban karamar hukumar Ideato North a jihar Imo Chris Ohizu.

Wakilinmu ya samu labarin cewa an fille kan shugaban karamar hukumar ne ranar Lahadi.

An tattaro cewa masu garkuwa da mutanen sun aikata wannan danyen aiki ne bayan da suka karbi kudin fansa N6m.

An yi garkuwa da Ohizu tare da wasu mutane biyu ranar Juma’a daga gidan sa da ke unguwar Imoko a yankin Arondizuogu. Gidan kasarsa ma gaba daya ya lalace.

An tattaro cewa an harbe shugaban karamar hukumar ne kafin a tafi da shi.

Wakilinmu ya ga faifan bidiyo na shugaban da aka yi garkuwa da shi, yana durkusa da wadanda suka yi garkuwa da shi suna gargadin Gwamna Hope Uzodimma cewa irin wannan kaddara na jiran sa.

An tattaro cewa bayan sun sare masa kai a ranar Lahadin da ta gabata ne suka sanya hoton bidiyon da wayarsa a matsayinsa na WhatsApp.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Imo, ASP Henry Okoye, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here