An gurfanar da wani mutum mai shekara 35 mai suna Temitayo Bamiro,a wata kotun majistare da ke Ojo ta jihar Legas bisa zargin lalata da ‘yarsa mai kimanin shekara 13.
Dansanda mai gabatar da kara, Simon Uche, ya bayyana wa kotu cewa, wanda ake zargin, ya aikata laifin ranar 7 ga watan Janairu a Ojo, da ke jihar Legas.
Kamar yadda dansanda mai gabatar da kara ya bayyana cewa, Bamiro, ya dade yana yin lalata da ‘yarsa.
Ya ce, wannan laifi ne da aka tanaji hukuncinsa a cikin sashin hukuncin aikata miyagun laifuka na jihar Legas.
Sai dai wanda ake zargin ya musanta zargin da ake yi masa.
Mai shari’a, Mista L.J.K. Layeni, ya mayar da kara zuwa hukumar kula da jin korafe-korafe domin neman shawarasu, saboda haka, sai ya dage sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Fabarairu sannan kuma ya bukaci a ci gaba da tsare Bamiro a kurkukun Badagry.