Mayakan ISWAP sun rarraba wa fasinjoji da dama Naira dubu dari-dari kyauta bayan sun tare su akan hanyar Maiduguri zuwa Mongono a jihar Borno ta Najeriya, a daidai lokacin da wa’adin daina amfani da tsohuwar Naira ke kara karatowa kamar yadda wani mazaunin yankin ya tabbatar wa RFI Hausa.
Mayakan sun tsaya akan titi dauke da buhunan tsaffin kudin da suka kunshi Naira 200 da 500 da kuma 1000 suna rarraba wa matafiyan da ke bulaguro akan hanyar.
Ita ma Jaridar Daily Trust da ake wallafa wa a Najeriya ta ce, mayakan na ISWAP sun yi shigar kayan sarki tamkar sojoji tare da girke motocin sulke guda 2 akan hanyar, inda suke tare motocin suna bin fasinjojin daya bayan daya da kyautar tsaffin kudin a babbar hanyar da ke karamar hukumar Guzamala.
 Wani da ke cikin fasinjan da suka samu wannan tagomomashi ya shaidawa manema labarai cewa mayakan na ISWAP sun baiwa kowanne fasinja da ke cikin motar kudin da yawansu ya kai dubu 100.
Wani fasinjan na daban ya bayyana cewa mayakan sun rika damkawa jama’a kudaden a hannunsu tare da fadin ‘‘kuje bankuna ku sauya su da sabbin kudade, Allah ya sa su zama masu amfani a gare ku’’.
Wannan dai ne karon farko da ake ganin irin wannan lamari a Najeriyar dai dai lokacin da jama’a ke fama da matsin rayuwa da kuma hauhawar farashin kayaki.
A lahadin da ta gabata ne dai babban bankin Najeriya CBN ya tsawaita lokacin amfani da tsaffin kudaden don baiwa jama’a damar kammala sauya takardun kudin da ke hannunsu.