‘Yan bindiga sun kai harin bam ofishin INEC

0
179

‘Yan  bindiga sun kaddamar da hari kan wani ofishin jami’an ‘yan sanda, yayin da suka jefa bam a ofishin Hukumar Zaben Kasar ta INEC a Karamar Hukumar Idemili ta Kudu da ke jihar Anambra ta Najeriya.

Kazalika maharan sun bindige wani karamin mai shekaru 16 har lahira a yayin kaddamar da farmakin a sanyin safiyar wannan Larabar.

Rundunar  ‘Yan Sandan Jihar ta tabbatar da harin, inda kakakinta DSP Toochukwu Ikenga ya ce, da misalin karfe 1 da minti 45 ne lamarin ya faru a cikin daren da ya gabata.

Tuni aka girke karin jami’an tsaro a sassan jihar domin dakile aukuwar wani harin.

Ba a karon farko kenan ba da ‘yan bindiga ke kai hari kan ofisoshin ‘yan sanda da na INEC a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here