Ku bayar da sabbin kudi ko mu kwace takardun shaidar mallakar ku – Zulum ga bankunan Borno

0
134

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya gargadi bankuna a jihar cewa su bayar da sabbin kudade a na’urorin cire kudi na ATM don rage karancin kudaden ga jama’a, idan ba haka ba kuma gwamnatin jihar za ta kwace takardun mallakar filayen bankunan har sai idan bincike ya tabbatar cewa matsalar daga bankin CBN take.

Zulum ya yi wannan gargadin ne a ranar Juma’a a Maiduguri lokacin da yake rangadin rassan bankunan, domin ganewa idonsa yadda karancin takardun sabbin kudin ya jefa jama’a cikin mawuyacin hali a jihar, ta hanyar dogayen layuka a ATM ya tsananta a cikin rashin tabbas.

“Duk wani banki a jihar Borno wanda yaki loda sabbin kudi a ATM dinsa, kuma bai damu da halin da jama’a suke ciki ba, tare da kin zuba isasshen kudi domin saukaka wa al’ummarmu radadin da suke ciki ba, to za mu soke takardar mallakarsu nan take. Face bankunan da bincike ya nuna suna da wata matsala ta daban.” in ji Zulum.

Kafin wannan matakin, Gwamna Zulum ya nuna rashin jindadin sa dangane da yadda daruruwan jama’a ke yin dafifi a layukan ATM a bankuna domin cire sabbin kudaden.

“Kamar yadda kuke gani a nan, maras gata ne kawai zaka iya gani a kan layi; ban ga masu kudi anan ba. Kuma an ce mutane da yawa suna nan tun karfe 3:00 na asuba, wasu ko abinci ba su ci ba. Sannan kuma da sabbi da tsoffin takardun Naira ba a samu, kuma hakan na yin illa ga harkokin kasuwanci a jihar Borno, saboda jama’a su na shan wahala.” Zulum ya nanata.

Gwamnan ya ci gaba da cewa: “Yanzu mun saki albashin kusan Naira biliyan 5 amma bankuna ba su da kudi, wasu na’urorin ATM din ba sa aiki. Kuma ba mu da matsala da manufar CBN ko ka’idar cire kudi, sun ce kowane mutum zai iya cire 20,000 a wuni, to amma me ya sa ba kowa ne zai iya samun wannan N20,000 ba?”

“A jiya ina garin Gubio mai yawan jama’a sama da 70,000 amma ba a iya samun Naira 100,000 a daukacin karamar hukumar, da sabbi da tsoffin kudin duka. Misali ragon 100,000 yanzu bai wuce 35,000 ba, saboda yadda ake neman kudi, al’amarin da ya jawo miyagun masu hannu da shuni na zuwa kauyuka don cutar talakawa.” Inji Zulum.

Gwamnan ya bukaci babban bankin Nijeriya (CBN) ya samar da sabbin takardun kudi a bankunan kasuwanci domin mutane su samu kudadensu.

“A yanzu haka a jihar Borno, na ziyarci na’urorin ATM a bankuna sama da goma amma babu kudi, mutane tsaye a layuka suna jiran tsammani.” in ji Zulum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here