Dalilin da ya sa taurarin da muke gani a sama ke raguwa duk shekara

0
139

Yawan taurarin da mutane ke gani da idanunsu yana raguwa a hankali cikin shekara 10 da ta gabata.

Wannan kuwa ya faru ne sakamakon hasken da ke mamaye samaniya na fitilun da muke kunnawa a duniya – kuma tun 2011 hasken da ake samu na fitilu a duniya ke karuwa a kowacce shekara.

Dakta Christopher Kyba, wani masanin kimiyya ne a cibiyar bincike kan duniya ta Potsdam da ke Jamus, ya shaida wa BBC cewa: ” Taurarin da muke gani na raguwa”.
Shi da abokan aikinsa sun wallafa wannan bincike a jaridarsu ta kimiyya.

Wannan shi ne karshen binciken wasu masu koyon nazarin ilimin taurari da masana kimiyya na tsawon shekara 12, wadanda suke fita da daddare suna kirga taurarin da ke sama.

Rahoton da mutanen suka kammala na intanet da ake kira Globe at Night, ya mayar da hankali kan sauyin da ake samu na ganin taurari a samaniya – kuma ya yi daidai da karin kashi 10 cikin 100 da ake samu na hasken duniya a kowacce shekara.

Wannan na nufin, yaron da aka haifa a yankin da ake iya ganin taurari 250 a sama, akwai yiwuwar nan da shekara 18 ba zai iya ganin ko taurari 100 ba a yankin.

Tiririn gurbatacciyar hasken duniya
Idan aka yi nazari kan bayanin da masu binciken nan Fabio Falchi da Salbador Bará, suka wallafa a jarida game da tiririn hasken duniya sun ce : “idan muka duba bidiyon da hukumar sararin samaniya take nunawa da kuma hotuna na duniyarmu da daddare, “Kyan hasken birane ne ke rudar mutane”, kai ka ce hasken bishiyar Kirsimeti ne.
“Ba su gane illar da ke cikin hoton ta gurbatar da hasken ke samarwa ba.
Kawai sun fi mayar da hankali ne kan kyan hoton da nau’in kalolin da suke da shi irin wanda ake gani a cikin ruwa, ba su lura da cewa tiririn gurbatattun sinadarai ne da ke tattare a cikin hasken wutar ba.
“Dakta Kyba, ya ce yana fatan ganin an samu ci gaba ta fuskar gurbatar da haske yake samar wa a ‘yan shekarun nan, saboda yawancin manyan birane suna sauya tsarin hasken da suke amfani da shi zuwa na makamashin da ba ya gurbata muhalli.
Garuruwa da birane musamman a kasashen da suka ci gaba, suna sauya fitilun kan titi zuwa masu aiki da hasken rana.
“Fatan shi ne idan za a yi amfani da wutar da ta dace, yanayin zai habaka ya yi kyau,” in ji shi.
Amma da wadannan fitilun da muke aiki da su – da yiwuwar mu sake gurbata hasken samaniyar da muke da shi.
Hukumar ta yi bayanin cewa “Cin karon da ake samu na hasken” da ake samu, ya sanya aka bullo da hasken da ake kira LED da alkawarin zai rage yawan amfani da makamashi, sannan kuma ya kara karfin gani ga bil’adama da daddare, amma hasken karuwa ma yake.
Idan aka samu cin karon da aka samu, shi ne a alkawarin sauki da kuma inganta kyau da zai yi, musamman ga al’umar da suka saba da hasken wuta.”Yawan hasken da ake samu shi ba iya illar rage taurari ya tsaya ba. Yana illa ga lafiyar dan ‘Adam da kuma tsarin yadda yake barci.
Yana haifar da matsala ga yanayin halayyar dabbobin da ba sa bacci da daddare, wanda a bayan nan wani bincike ya nuna ana samun raguwar kwari.
Shi tiririn hasken asara ce ga makamashi. Kuma kullum ci gaba muke da haska makamashi cikin sammai, wanda hakan ba daidai ba ne, in ji Daktan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here