Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya gana da mataimakan shugabannin jami’o’in tarayya gabanin babban zaben 2023.
A halin da ake ciki, shugaban na INEC ya jaddada cewa zaben 2023 zai gudana kamar yadda aka tsara.
Yakubu ya bada wannan tabbacin ne a wata ganawa da ya yi da mataimakan shugabannin jami’o’in tarayya a ranar Alhamis.
Ya kuma bukaci mataimakan shugabannin da su yi cikakken bincike domin kaucewa daukar ma’aikatan da ke da alaka da jam’iyyun siyasa da tarihin bangaranci kafin mika sunayensu ga hukumar.
Shugaban na INEC ya kuma ba da tabbacin cewa za ta fara gudanar da nata binciken sunayen da jami’o’in suka tura domin gudanar da zaben.
Yakubu ya kawar da fargabar da wasu daga cikin VC suke da shi na rashin tsaro, yayin da ya tabbatar da cewa an tsara tsare-tsare masu inganci don kare lafiyar dukkan ma’aikata, kafafen yada labarai, ’yan kungiyar matasa da sauran jami’an zabe.
A cewarsa, adadin masu kada kuri’a (sama da miliyan 93) na zaben 2023 ya fi wadanda suka yi rijista a Afirka.