Sanatan jihar Delta ya fara zaman gidan yari bayan EFCC ta kama shi

0
111

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya ta ce, Sanata Peter Nwaoboshi da ke wakiltar mazabar jihar Delta ta Arewa, yanzu haka ya isa gidan yarin Ikoyi domin zaman sarka na shekaru 7 kamar yadda kotu ta yanke masa hukunci, saboda samun sa da laifin zamba cikin aminci na kudin da ya kai Naira miliyan 805.

Wannan ya biyo bayan nasarar da jami’an EFCC suka samu na cafke Sanatan wanda ya shiga wasan-buya da su tun bayan da kotu ta yanke hukunci akan shari’rar da aka masa a shekarar da ta gabata.

Mai magana da yawun hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya ce jami’ansu sun yi nasarar cafke ‘dan majalisar dattawan ne a wani asibiti da ke Lagos a ranar Litinin da ta gabata, kuma nan take aka tasa keyarsa zuwa gidan yarin Ikoyi kamar yadda kotu ta bada umurni.

Idan ba a manta ba a ranar 1 ga watan Yulin bara, kotun daukaka kara da ke Ikoyi ta samu Sanatan da laifin halarta kudaden haramun da kuma zamba cikin aminci, inda ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 7 da kuma rufe kamfanoninsa guda 2 wadanda aka mallaka wa gwamnatin tarayya.

Tun bayan yanke hukuncin, Sanata Nwaoboshi ya shiga wasan buya da jami’an tsaro da ke neman kai shi gidan kaso har zuwa ranar litinin da dubunsa ta cika.

Yayin da yake boye, ‘dan majalisar dattawan ya ruga kotun koli domin ganin ta yi watsi da hukuncin kotun daukaka karar, amma sai alkalai suka yi watsi da bukatar a ranar 27 ga watan Janairun da ya gabata.

Alkali Emmanuel Agim da ya jagoranci hukuncin ya bayyana bacinsa da yadda Sanatan yaki mutunta doka, yake kuma bukatar kotu ta sake nazari akan hukuncin.

Yayin da yake tsokaci lokacin yanke hukuncin, alkali Tijani Abubakar ya ce ya zama wajibi su nunawa ‘yan Najeriya cewar babu wanda yafi karfin doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here