‘Yan Najeriya sun jinjina wa kotun koli da ta dakatar da shirin CBN

0
64

‘Yan Najeriya na ci gaba da jinjina wa Kotun Kolin Kasar saboda hukuncin da ta yanke na tilasta wa Babban Bankin Kasar, CBN na watsi da wa’adin ranar 10 ga watan nan na dakatar da amfani da tsoffin kudaden da aka sauya wadanda karancinsu ya haifar da matsaloli baki daya.

Jama’ar kasar daga sassa daban-daban ciki har da talakawa da shugabanni da kuma malaman addinai sun bayyana korafinsu kan yadda aka samu matsala wajen sauyin, yayin da bankuna suka gaza samar da sabbin kudaden da ake bukata.

Wannan matsala ta sa aka fara samun bore a wasu biranen kasar da kuma kai hari a wasu bankuna, abin da ya kai ga rasa rai a birnin Abeokuta ta Jihar Ogun.

Ko a birnin Ibadan, sai da ‘yan sanda suka tarwatsa gungun matasan da suka yi zanga-zanga domin nuna bacin ransu da karancin sabbin kudaden a bankuna, yayin da jama’a ke tururuwa domin neman su a bankuna.

Wannan ta sa gwamnonin jihohin Kaduna da Zamfara da kuma Kogi rugawa kotun kolin domin gabatar da bukatar haramta wa babban bankin damar dakatar da wa’adin sauyin kudin da ya gindaya na ranar 10 ga watan Fabarairu.

Dan takarar shugaban kasar Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa da matakin, yayin da yake cewa, Najeriya ta kama hanyar fadawa cikin rudani da rashin tabbas dangane da abin da ya shafi tattalin arzikin kasa da kuma siyasa sakamakon irin matakan da babban bankin ya dauka.

Tinubu ya ce kasashen da suka ci gaba kan bada wa’adin watan 12 domin gudanar da irin wannan aiki na sauya kudin, yayin da ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su sake zama domin sake fasalin aikin ta yadda babu wani dan Najeriya da zai koka.

Ita ma Hukumar Bada Lamuni ta Duniya ta bukaci kara wa’adi ga jama’a domin ba su isashen lokacin sauya kudaden nasu, yayin da take cewa lokacin da babban bankin ya dauka ya yi kadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here