Gwamnatin Kano ta ba wa ’yan magani mako 2 su bar kasuwar sabon gari

0
135

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa masu sayar da magani da ke kasuwar Sabon Gari da sauran wurare a birnin Kano, wa’adin mako biyu su koma sabuwar kasuwar magungunan da gwamnati ta gina.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin bikin bude sabuwar kasuwar, in da ya ce ita ce kadai halastacciyar kasuwar magani da gwamnati ta amince da ita a yanzu a Jihar, don haka za ta rufe sauran.

wannan ce kadai halastacciya a yanzu, duk wanda muka samu ya saba umarnin, za mu dau mataki a kansa,” in ji Ganduje

Shi ma Shugaban Kungiyar Masu Harhada Magunguna ta Najeriya Ibrahim Babashehu Ahmad ya yi makamancin wancan gargadin, inda ya ce sashin tabbatar da doka na kungiyar zai tabbatar da rufe duk wani shago da ya yi taurin kan kin bin umarnin.

Shi ma dai Ministan Lafiya, Osagie Ehanire ya ce kasuwannin Sabon Gari da sauran manyan shagunan da ke sayar da magunguna a jihar, na taimakawa wajen karuwar magungunan jabu da miyagun kwayoyi, kuma zuwan kasuwar zai magance hakan.

Kasuwar dai ita ce irinta ta farko da aka kammala ginawa a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here