Rikici ya barke a Lagos saboda karancin Naira

0
157

Ana zaman tankiya a yankin Ikorodu na jihar Legas da kewayensa, biyo bayan rikicin da ya barke a kasuwar Mile 12 da safiyar Juma’ar nan, rikicin da aka ce ya barke saboda karancin Naira.

Mile 12  dai shahararren kasuwa ce ta kasa da kasa, inda ake sayar da kayayyakin abinci.

Ganau sun ce an yi harbe harbe, lamarin da ya  sa akasarin ma’aikata da suke kan hanyarsu ta zuwa wajen aiki suka koma gida, musamman ma wadanda ke fita wajen Ikorodu.

Rikicin ya bazu zuwa ungwannin Ketu da Ojota, wadanda ke kan hanyar Ikorodu, sai dai rahotanni sun ce an tura  sojoji wuraren don dakile yaduwar rikici.

Majiyoyi sun ce rikicin na da nasaba ne da karancin Naira  da ya ki ci ya ki cinyewa, abin da ya haddasa nakasu ga harkokin kasuwanci, ya  kuma gurgunta galibin ‘yan Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here