Zulum ya ba wa ‘yan sanda kyautar motocin sulke 9

0
90

Gwamna Babagana Umara  Zulum ya mika wa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno motocin yaki masu sulke guda tara domin kara karfinsu wajen dakile laifuka da kuma mayar da martani cikin lokaci ga ayyukan ta’addanci a jihar.

Zulum ya yaba wa rundunar da sauran jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen yakar ’yan Boko Haram da kuma hana sauran laifuka a kananan hukumomi 27 na jihar.

Ya kuma yi alkawarin karin motocin sulke da sauran tallafi ga ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da ke aikin dawo da zaman lafiya a jihar.

“Gwamnatinmu za ta ci gaba da baiwa ’yan sanda goyon baya don cimma manufofinsu na kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa,” in ji Zulum.

Aminiya  ta ruwaito cewa, a cikin kusan shekaru hudu gwamnatin jihar ta ba tallafin motocin sintiri sama da 1,300 gwa hukumomin tsaro da suka hada da ’yan sanda, DSS, Civilian JTF, mafarauta da ’yan banga a fadin jihar.

Gwamnan ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa jajircewarsa wajen yaki da masu tada kayar baya wanda ya taimaka matuka wajen samun zaman lafiyar Jihar Borno.

“Mu a Borno, babu abin da za mu ce face mu gode wa Gwamnatin Tarayya karkashin Shugaba Muhammadu Buhari bisa dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

“Wannan ba zai taba yiwuwa ba sai da goyon bayan sojojin Najeriya, ’yan sandan Najeriya, DSS, NSCDC, jami’an tsaro da masu aikin sa kai,” in ji Zulum.

Zulum ya kuma yaba wa shugaban ’yan sanda, Alkali Baba Usman bisa irin kokarinsa ba dare ba rana don ganin harkokin tsaro sun inganta a jihar ta Borno da ma kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here