Hukumar dake kula da jami’o’i ta kasa NUC ta bada shawarar yiwa jami’o’i tsari na musamman ta yadda za a fitar da su daga matsalar karancin laccarori.
Hukumar na cewa kimanin laccarorin dubu dari ne ke daukar daliban jami’o’i sama da milyan biyu.
Hukumar NUC ta bayyana hakan ne ta cikin wani daftarin baya-bayan nan da ta fitar.
- Ba a fara siyar da fom ba – hukumar JAMB
- Kuyi amfani da FCAPT wajen bunkasa noma – Farfesa Sharubutu
Mataimakin shugaban hukumar bangaren mulki Mista Chris Maiyaki da ya bayyana hakan a cikin daftarin, ya kara da cewa hukumar NUC na kula da jami’o’i sama da dubu dari biyu, da suka hada da 48 mallakin Gwamnatin tarayya da 54 mallakin Gwamnatocin jihohi da kuma 99 masu zaman kansu.
“Idan aka kula sosai, bangaren na da kiyasin sama da dalibai milyan 2 da ma’aikata dubu dari da saba’in (wanda ba masu koyarwa ba) da kuma masu koyarwa dubu dari.
“Matsalolin da suka dabaibaye bangaren basu wuce rashin wadatattun kudin gudanarwa ba, karancin kasafi, karancin wutar lantarki da kuma na ma’aikatan ma.
“Hakan ya zama wajibi a tsame su daga sabon tsarin da Gwamnatin tarayya ta hau na daukar aiki, idan ana so suyi gogayya da takwarorinsu na duniya baki daya,” Maiyaki.