A yau Talata ne sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, zai fara ziyarar kwanaki biyu a Najeriya.
A yayin ziyarar tasa zai kai ziyara jihar Borno in da zai gana da gwamnan jihar Babagana Umara Zulum, da kuma iyalan wadanda rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar rasa rayukansu.
Majalissar Dinkin Duniya zatai zama na musamman kan Kasar habasha
Kazalika sakatare janar din zai kuma gana da shugabannin addinai da na kungiyoyin mata da matasa da kuma shugabanin kamfanoni masu zaman kansu.
Baya ga wadannan mutane da zai gana da su zai kuma gana da jami’an diflomasiyya da ma wadanda ke sansanonin yan gudun hijra a jihar Borno.