Ma’aikatan kula da zirga-zirgar jiragen sama sun hana tashin jirage a Kano

0
61
Tashi da saukar jirage ya samu tasgaro a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano MAKIA, sakamakon zanga-zanga da ma’aikatan hukamar da ke kula da zirarg- zirgar jirgin sama ta kasa ke yi.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa jiragen da za su tashi yau Litinin ba samu damar tashi ba sakamakon rikicikin.
Jiragen da basu samu damar tashi ba sun hada da AZMAN da kuma Max Air da ya kamata su tashi zuwa Abuja da Lagos.
Wannan jaridar ta gano cewa manyan mutane da dama abin ya rutsa dasu, wadan da suka hada da ‘yan majalisu da mataimakan gwamnoni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here