Rushewar katangar makaranta ta kashe yara 2 a Legas

0
69
Wasu yara biyu, Samat Saheed da wata yarinya da ba a fayyace sunanta ba, sun rasa rayukansu a lokacin da katangar makarantar Covenant Point Academy ta rufta musu, a titin Ajose da ke unguwar Amukoko a Jihar Legas.
Jaridar PUNCH Metro ta tattaro cewa yarinyar mai shekara 9, ta zo wuce wa ne ta gaban makarantar, inda shi kuma Samat mai shekaru 3 ke wasa a jikin katangar, kusa da shagon mahaifiyarsa a lokacin da ta rushe a kan su.
Wakilim jaridar ya tattaro cewa, a lokacin da katangar ta danne kananan yaran, sai ta danne kan Samat, inda nan take ya mutu, yayin da yarinyar ƴar shekara tara ta fita daga hayyacinta, kuma rahotanni sun ce ta mutu jim kadan da faruwar lamarin a asibiti.
Da yake zantawa da manema labarai, wani ganau, Ganiyu Ayeloja, ya ce mazauna garin da lamarin ya faru sun sanar da ƴan sanda, inda ya ce an kama mai makarantar.
Shi ma jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here