Nan ba da dadewa ba, matsalar tsaro zata zama tarihi – Buhari

0
84

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa dubi da yadda dakarun sojin Najeriya suka kara kaimi wajen yakan yan bindiga, matsalar tsaro zai zama tarihi nan ba da dadewa ba.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne ranar Asabar a New York, birnin Amurka yayin zama da Firai Ministan kasar Ireland, Michel Martin.

A jawabin da mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya fitar ranar Asabar, yace: “Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma’a a New York ya bayyana cewa bisa yadda Sojojin Najeriya ke kokari, matsalar tsaro zata zama tarihi nan da lokaci kadan.”

“Shugaba Buhari ya ce a watannin baya-bayan nan, kokarin da sojojin Najeriye keyi na nuna cewa muna hanyar shawo kan matsalar rashin tsaro.”

“Zamu cigaba da hada akai da kasashen duniya wajen amfani da fasaha saboda Najeriya ta amfana.”