An tsinci gawar dattawan ne bayan sun fara rubewa, da saran adda a jikinsu, a ranar Alhamis a garin Nnewi da ke Jihar Anambra.
An gano gawarwakin ne bayan wari ya addabi makwabta a unguwar Abubor Nnewichi-Nnewi ne suka yi ta neman inda warin ke fitowa.
Aminaya ta samu rahoto cewa matashin yana ta’ammali da miyagun kwayoyi, kuma ya kashe iyayen nasa ne bayan wata takaddama, saboda sun hana shi kudin da ya bukata.
Mazauna unguwar Abubor Nnewichi-Nnewi sun yi zargin sai da ya kashe mahaifan nasa sannan ya tsere zuwa inda ba a sani ba kwana uku da suka gabata.
Kakakin ’yan sandan Jihar Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, ya ce saran adda da aka samu a jikin gawarwakin alama ce ta an nuna musu rashin imani.
A cewarsa, an tura lamarin zuwa babban sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin gudanar da zuzzurfan bincike.
(AMINIYA)