An yanke wa wani dan sanda hukuncin daurin rai da rai a Legas

0
17

Wata babban kotun Jihar Legas, ta yanke wa wani korarren dan sanda Olalekan Ogunyemi, daurin rai dai rai saboda kashe wani mai wanda ya zo kallon kwallon kafa, Kolade Johnson.

Ogunyemi, wanda ke aiki tare da tawagar yaki da yan kungiyar asiri na yan sanda, ya bindige Johnson a cikinsu a ranar 31 ga watan Maris na 2019 a wurin kallon kwallo a Mangoro, Ikeja, Legas.

Yayin yanke hukuncin, Mai shari’a Adenike Coker ta samu wanda aka yi karar da laifin da aka tuhume shi da shi ta kuma yanke masa hukuncin daurin rai da rai, inda ta ce dole ya yi a kalla shekaru 25 a gidan yarin.

Alkaliyar ta kuma yanke wa korarren dan sandan hukuncin daurin rai da rai bisa kisa amma ba na ganganci ba.

Olalekan wanda da farko aka gurfanar da shi kan gisar gilla, amma kotun ta same shi da kisa ba da niyya ba.

Yayin shari’ar, masu binciken sun kira shaidu bakwai yayin da wadanda aka yi karar suka kira shaidu biyu.

Yayin shari’ar, wani likita Dr Oluwaseun Williams, ya bada shaida cewa, an harbi Johnson, dan shekara 35 sai shida.