Ya kamata Atiku ya daina sa ran zama Shugaban Kasa tun yanzu – Tinubu

0
108

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwuju Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwara tun a yanzu takwaransa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya fidda ran zama Shugaban Kasa.

Tinubu ya yi wannan gargadin ne a yayin da jam’iyyun kasar ke shirye-shiryen fara yakin neman zabensu a makon gobe.

Tinubu wanda ya mulki Jihar Legas tsawon waadi biyu, ya ce a yanzu da Atiku ya gasa warware matsalar rikicin cikin gida da ta dabaibaye jam’iyyar PDP, ya nuna ba zai kai labari ba a Zaben 2023.

Cikin wata sanarwar da Darektan Labarai da Hulda da Al’umma na Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce rikicin cikin gida da jam’iyyar PDP ke fama da shi a yanzu ba wani ba nae ya haddasa face Atiku.

Sanarwar ta ce dagewar da Atiku ya yi kan cewa lallai sai dan takara daga yankin Arewa ne zai kawo wa jam’iyyar nasara ita ce musabbabin matsalar da suke fuskanta a yanzu.

A cewar sanarwar, “yunkurin da tsohon Mataimakin Shugaban Kasar yake yi na neman zama Shugaban Kasa wata dama ce da za ta sake subuce masa.

“Wannan dai na faruwa ne a kan idonmu tun ma kafin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bude kofar fara gudanar da yakin neman zabe.

“Jam’iyyarsa ta PDP tana cikin rudani. Al’amura sun kara dagule wa Wazirin Adamawa, la’akari da yadda wani rahoto da Sashen Binciken Tattalin Arziki ya yi hasashen zai kara shan kasa a zabe mai zuwa.

“Atiku ya saba wa ka’idojin jam’iyyarsa kan tsarin karba-karbar mulki tsakanin Arewa da Kudu.

“Ya yi kane-kane wajen kwace tikitin takarar jam’iyyarsa ba tare da la’akari da tsari da al’adun kasar ba.

“A yanzu dai rudanin da jam’iyyar PDP ke ciki ya nuna Atiku ya fara girbar abin da ya shuka tun kafin a je ko’ina.”