NDLEA ta kama wani tsoho mai shekaru 75 da tabar wiwi 49Kg da kodin mai nauyin 733Kg a Kano

0
75

Jami’an tsarol sun kama wani tsoho mai shekaru 75 bisa laifin mallakar tan din haramtattun kwayoyi” a unguwar Anguwan Sate, yankin karamar hukumar Mayo Belwa a jihar Adamawa.

Daraktan yaɗa labarai na hukumar NDLEA Femi Babafemi ne ya bayyana haka a ranar Lahadi a yayin da yake gabatar da jawabi kan ayyukan hukumar a fadin kasar nan, ya ce an gano wani tsoho mai shekaru 75 da haihuwa mai suna Usman Bahama wanda aka fi sani da Clement wanda ya mallaki gonakin tabar Wiwi da ya mallaka, wanda aka gano 49kg tabar da aka kama shi a ranar 20 ga watan Satumba.

Haka zalika an kwato kwali guda 979,119 na ‘Pregabalin’ da ya kare mai nauyin kilogiram 733 daga hannun Musbahu Ya’u guda 28 da kuma wasu biyar a Unguwar Dansarai a Kano,” in ji Babafemi.

Babafemi ya ce hukumar ta kuma kama kwalabe miliyan 1.01 da capsules na tramadol da “Akuskura, maganin da aka haramta kwanan nan.

An kone hecta 10 na gonakin Akuskura a Edo da Adamawa, sannan an kama 2,536kg na Tabar wiwi.