Buhari ya yabawa sojojin da suka kwato fasinjojin jirgin kasa na Abuja-Kaduna

0
97

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjinawa sojojin kasar akan rawar da suka taka wajen kubutar da sauran fasinjojin jirgin kasar da akayi garkuwa da su watanni 6 da suka gabata.

Buhari ya yabawa sojojin ne lokacin da ya ziyarci asibitin sojin cibiyar horas da kananan hafsoshin sojin NDA dake Kaduna, inda aka tantance lafiyarsu.

Mai Magana da yawun shugaban Garba Shehu yace Buhari ya bayyana farin cikinsa da yadda sojojin suka kubutar da sauran fasinjojin 23 ba tare da wani ya jikkata ba.

Cikin wadannan mutane da suka kwashe watanni 6 a hannun Yan ta’addan harda karamar yarinya mai kasa da shekaru 3 da kuma wasu ma’aikatan jirgin.

Shugaban ya kuma yabawa kwamitin da suka yi aikin kubutar da mutanen wanda Babban Hafsan sojin kasa Laftanar Janar Lucky Irabor ya kafa a karkashin jagoran Janar Usman Abdulkadir mai ritaya.

Sauran Yan kwamitin sun hada da Janar Adamu Jalingo da Janar Abubakar Saad da Dr Murtala Ahmed Rufai da Ibrahim Abdullahi da Ambasada Ahmed Magaji, sai kuma Sakataren su Farfesa Usman Yusuf.

Yan uwa da iyalan sauran fasinjojin da Yan ta’addan suka kwashe sun biya makudan kudade kafin samun kansu daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.