OPEC ta zabtare yawan man da Najeriya za ta rika fitarwa kasuwannin Duniya

0
52

Kungiyar OPEC ta kasashe masu arzikin man fetur ta zabtare adadin man da ta baiwa Najeriya ta dinga fitarwa kowacce rana daga ganga miliyan 1 da dubu 826 kowacce rana zuwa ganga miliyan guda da dubu 742.

Bayan wani taro da kungiyar ta gudanar domin daidaita farashin man wanda ya fadi kasa da Dala 90 a kasuwanni duniya makon jiya, OPEC tace Najeriya zata dinga fitar da ganga miliyan guda da dubu 742 daga watan Disamba mai zuwa, yayin da aka ragewa Sudan nata zuwa ganga dubu 72.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalolin cikin gida wajen samar da man da ake bukata, sakamakon yadda barayi ke fasa bututun man suna sace shi.

Sanar da daukar wannan mataki da OPEC tayi ya sanya farashin man Najeriya da ake kira ’Bonny Light’ ya tashi nan take zuwa Dala 93 da Centi 36 kowanne ganga, sabanin yadda kasar tayi kasafin kudin ta akan Dala 62 na farashin man.

Gwamnatin Najeriya ta ja kunnen hukumomin tsaron kasar akan yadda ake fama da matsalar satar man, wanda kamfanin NNPC yace yana asarar akalla ganga dubu 400 kowanne mako.