Ana fargabar mutane 33 sun mutu a Jihar Neja bayan kifewar kwale-kwale

0
59

Akalla mutane 33 ake fargabar sun mutu daga cikin wasu fasinjojin kwale kwale sama da 50 da suka nitse a ruwa sakamakon kifewar jirgin ruwan da suke ciki a Jihar Neja.

Rahotanni sun ce kwaler kwalen ya kife ne tsakanin kauyen Danchitagi dake karamar hukumar Lavun zuwa Gbara dake karamar hukumar Mokwa a cikin daren jiya juma’a.

Bayanai sun ce daga cikin mutanen 33 da suka nitse akwai mata da yara kanana tare da kayayyakin miliyoyin nairori bayan cin kasuwar Danchitagi, yayin da wasu kuma suka fito daurin aure daga wasu unguwanni.

An ceto mutane 17

Mazauna yankin sun shaidawa Jaridar Daily Trust cewar daga cikin mutane sama da 50 dake kwale kwalen, 17 kawai aka ceto, yayin da sauran suka bata.

Daya daga cikin masu aikin ceto a wurin yace sun yanke kaunar samun wani daga cikin wadanda suka bata da rai, ganin dogon lokacin da aka dauka da kuma zurfin ruwan.

Akasarin wadanda hadarin ya ritsa da su mazauna kauyukan bakin ruwa ne dake Muregi da Gbara da Ghazhe da Tadima.

Mutanen da ke ciki sun kai 60

Shugaban agajin gaggawa na jihar Neja Ibrahim Inga ya tabbatar da aukuwar hadarin ba tare da gabatar da adadin mutanen da suka mutu ba, yayin da hakimin Gbara Alhaji Mohammed Saba yace mutanen dake cikin kwale kwalen sun kai 60.