Duk wanda zai gaji Buhari ya shirya gadar bashin Naira Tiriliyan 39 – Masana

0
50

Masana tattalin arzikin a Najeriya sunyi gargadin cewa duk Wanda zai Gaji shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shirya gadar bashin Naira Tiriliyan 39 da doriya.

A tsawon shekara 7 da rabi shugaban Kasa Buhari ya ciwo bashin naira tirilyan 31 tare da neman Kari anan gaba.

Masana tattalin arzikin sun nemi masu son gadar gwamnatin Shugaba Buhari tun yanzu su fara tunanin yadda zasu warware matsalolin bashin da ake bin Najeriya da Kuma yin tunanin yadda zasu Kara Maida hankali wajen samun kudaden shiga na cikin gida Maimakon yawan dogaro da ciwo bashi.

Zuwa watan Mayu da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai mika mulki ga sabuwar gwamnati a kasar nan ,ya gabatar da kudi sama da naira Tiriliyan 93 a matsayin kasasin kudi na shekaru 8 da yayi yana mulkin kasar nan.

Daga cikin kasafin kudi sama da naira Tiriliyan 93 daga shekarar 2016 zuwa 2023 da shugaba Buhari zai sauka,an ware sama da naira Tiriliyan 64 domin yin manyan ayyuka ciki harda biyan albashin ma,aikata da biyan albashin yan majalissun tarayya.

A shekarar 2016 shugaban kasa Buahri ya gabatar da naira Tiriliyan 6 da doriya ne kacal a matsayin kasafin kudin shekarar,daga nan sai ya karu zuwa Tiriliyan 7 da rabi a shekarar 2017 sai ya koma Tiriliyan 9 da rabi a shekrar 2018.

A shekarar 2019 ya dawo kasa zuwa naira Tiliyan 8 da miliyan dubu dari 9 sai kuma ya sake komawa sama zuwa naira Tiliyan 10 da rabi a shekarar 2020 a tsakanin shekarar 2021 zuwa 2022 kasafin kudin kasar nan yayi tsalle ya koma sama da naira Tiriliyan 13 da rabi sai kuma kasafin karshe da shugaban ya gabatar na shekarar 2023 ya tasamma sama da naira tirliyan 17,wanda yanzu ma gwamnatibn tarayya tace sai ta ciwo bashin sama da naira tiliyan 8 domin cike gibin kasafin na shekarar 2023.

A watan Agustan da ya gabata ne Bankin Duniya ya sanya Najeriya cikin jerin kasashe 10 mafiya shiga hadarin karbar bashi a duniya ,inda Najeriya ta zamo ta Biyar.

kuma zuwa yanzu kasashen duniya suna bin Najeriya bashin sama da Dala miliyan dubu 11 da dala miliyan dari 7.

Kasar Indiya itace tafi kowacce kasa cin bashi a duniya sai kasar Bangaladash ta biyu sai Pakistan ta uku sannan sai Vietnam ta hudu Najeriya ta biyar.

PUNCH.