Karim Benzema ne gwarzon kwallan kafa na duniya

0
114

Karim Benzema ya lashe kyautar Ballon d’Or ta Gwarzon dan wasan kwallon kafa ta duniya na 2022, yayin bikin da ya gudana a birnin Paris, inda ya gaji Lionel Messi wanda ya lashe kyautar a bara.

A shekarar bana dai, Paris babban birnin Faransa ya zama na musamman ga dan wasan gaban na Real Madrid, domin kuwa a nan ne,  suka lashe kofin gasar Zakarun Turai karo na 14, bayan doke Liverpool da 1-0 a watannin baya.

Kididdiga ta nuna cewar, sau goma sha biyu aka baiwa ‘yan wasan Real Madrid kyautar Ballon d’Or, wanda yayi daidai da adadin da ‘yan wasan Barcelona suka samu.

Tsofaffin ‘yan wasan Real Madrid da suka samu kyautar gwarzon dan wasan a baya sun hada da Alfredo Di Stefano da Raymond Kopa da Luis Figo da Ronaldo Nazario da Fabio Cannavaro da Cristiano Ronaldo da kuma Luka Modric.

Benzema wanda ya taka rawar gani a gasar zakarun Turai a kakar wasan da ta wuce, shi ne dan wasan Faransa na farko da ya lashe kyautar ta Ballon d’Or tun bayan Zidane a shekarar 1998.

Sadio Mane ne ya zo na biyu, sai Kevin de Bruyne na uku, yayin da Robert Lewandowski ya zo na hudu.

Courtois ya yi wa masu tsaron raga zarra, Mane ya lashe kyauta ta musamman

A bangaren masu tsaron raga kuwa, golan Real Madrid Thibaut Courtois ne ya lashe kyautar zama Gwarzo, la’akari da gagarumar gudunmawar da ya baiwa kungiyarsa yayin wasanni mafiya hatsari da ta buga a kakar wasan da ta gabata, musamman yayin karawa da Liverpool a wasan karshe na gasar Zakarun Turai.

Kyauta ta musamman don karrama wanda ya fi gudanar da ayyukan jin kai, an mika ta ne ga dan wasan gaban Bayern Munich da  Senegal Sadio Mane, bisa irin gudun mowar da yake bayarwa ga rayuwar jama’a.

Dan wasan tsakiya na Barcelona da Spain Gavi, ne ya lashe kyautar matashin dan wasa mafi hazaka.

Mancester City ce gwarzuwar kungiya ta shekarar 2022

Wannan ya dogara ne akan City da ke da mafi yawan ‘yan wasan sunayen su ya fito a bangarori daban-daban na wannan kyauta.

Liverpool ke biye mata a mataki na biyu, sai Real Madrid da ta kasance a matsayi na uku.