Gwamnatin tarayya ta tabbatar da kammala aikin gadar Neja ta biyu

0
81

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da kammala aikin gadar Neja ta biyu kuma nan ba da jimawa ba za a bude wa masu ababen hawa su fara amfani da su.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gabatar don gabatar da katin zabe na shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja ranar Laraba.

A cewar ministan, abin da ya kawo tsaiko wajen kaddamar da aikin shi ne gina titin hanyar, wanda ambaliyar ruwa ta kawo cikas.

Fashola ya ce, “Ina iya tabbatar da cewa gadar Neja ta biyu ta kammala. Mutane na iya tafiya ta cikin gadar yanzu ba tare da fargaba ba. Abin da ya rage shi ne hanyar mai tsawon kilomita hudu ta gefen Asaba.

“A yanzu haka, injin mu yana nan, dole ne mu sake gina titin tare da dawo da kasar da ambaliyar ruwa ta yashe a baya-bayan nan. A bangaren Onitsha kuma akwai titin kilomita bakwai da ta hada gadar da kuma hanyar Onitsha zuwa Owerri.”

An dai jima ana sa ran za a kammala gadojin wanda suka shafe tsawon shekaru ana dakon kammala su.