HomeLabaraiZan kammala aikin wutar mambila idan aka zabe ni - Tinubu

Zan kammala aikin wutar mambila idan aka zabe ni – Tinubu

Date:

Related stories

Yadda lamari ya kasance yayin zuwan Buhari Kano don kaddamar da aiyuka 8

An tsauraran matakan tsaro a cikin birnin Kano da...

Najeriya ta yi asarar likitoci 2800 a cikin shekaru biyu – NARD

Shugaban kungiyar likitocin Najeriya NARD, Dr Innocent Orji ya...

Yadda ake canzar da kudin Sepa zuwa Naira a yau Litinin

Farashin Separ Nijar zuwa Naira a farashin kasuwar canjin...

Yadda ake canzar da kudin Fam zuwa Naira a yau Litinin

Darajar musayar Naira da Fam bisa bayanan da aka...

Yadda ake canzar da kudin Yuro zuwa Naira a yau Litinin

Farashin bakar kasuwar Yuro zuwa Naira a yau,30 ga...

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin kammala aikin wutar lantarki na Mambila da gwamnatin Buhari ta ce tana aiki a kan sa.

Tinubu ya kuma yi alkawarin shawo kan matsaloli da arewacin Nijeriya ke fuskanta da kuma kasar baki daya da zarar ya zama shugaban kasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi a wani taro da kungiyoyi masu fada aji na arewacin Nijeriya suka hada da kungiyar dattawan Arewa suka shirya wa ‘yan takarar shugaban kasa a JIhar Kaduna.

Tinubu ya ce cikin abubuwan da zai fara yi shi ne kammala aikin wutar Mambilla da aka shafe tsawon shekaru ba tare da yin aikin ba, inda ya ce tashar za ta samar wa da kasar wuta mai karfin megawatt 3,050 wanda kuma zai kasance daya daga cikin tasha mafi girma a fadin kasar.

“Abin da yake kawo jinkirin kammala wannan aikin shi ne rashin isassun kudade. Ba a ware isassun kudade ga manyan ayyuka masu daukar dogon lokaci. Za mu kammala wadannan aiki saboda muna zuwa da wani tsari mai kyau ga kasar nan,” in ji Tinubu.

Ya kuma ce zai kawo masu zuba jari a ciki da kuma wajen kasar wadanda za su kammala aikin da zai kawo wa kasar ci gaba.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories