HomeLabaraiGwamnatin tarayya ta tabbatar da kammala aikin gadar Neja ta biyu

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da kammala aikin gadar Neja ta biyu

Date:

Related stories

Ina addu’ar Allah ya saukar min da cutar da za ta sa na shiryu – Murja Ibrahim Kunya

Fitacciyar mai barkwancin nan ta manhajar TikTok, Murja Ibrahim...

2023: Na rasa laifin me na yi wa mutanen da suke cin amana ta — Tinubu

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed...

Hattara da masu yada labaran karya a kan Tinubu — APC

Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na APC, ya...

Majilisar wakilai tayi watsi da sabon wa’adin da CBN ta kara

Kwamitin Adhoc na Majalisar Wakilai kan sabbin tsare-tsare na...

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da kammala aikin gadar Neja ta biyu kuma nan ba da jimawa ba za a bude wa masu ababen hawa su fara amfani da su.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gabatar don gabatar da katin zabe na shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja ranar Laraba.

A cewar ministan, abin da ya kawo tsaiko wajen kaddamar da aikin shi ne gina titin hanyar, wanda ambaliyar ruwa ta kawo cikas.

Fashola ya ce, “Ina iya tabbatar da cewa gadar Neja ta biyu ta kammala. Mutane na iya tafiya ta cikin gadar yanzu ba tare da fargaba ba. Abin da ya rage shi ne hanyar mai tsawon kilomita hudu ta gefen Asaba.

“A yanzu haka, injin mu yana nan, dole ne mu sake gina titin tare da dawo da kasar da ambaliyar ruwa ta yashe a baya-bayan nan. A bangaren Onitsha kuma akwai titin kilomita bakwai da ta hada gadar da kuma hanyar Onitsha zuwa Owerri.”

An dai jima ana sa ran za a kammala gadojin wanda suka shafe tsawon shekaru ana dakon kammala su.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories