An sanya dokar ta baci a kasar Chadi saboda zanga-zanga

0
95

Kusan mutum 50 ne suka mutu, inda daruruwa suka jikkata, a zanga-zangar da ke wakana a kasar Chadi.

Gwamnatin kasar yanzu haka ta sanya dokar hana zirga-zirga a fadin kasar, domin shawo kan matsalar.

Firayim Ministan Chadi Saleh Kebzabo, a ranar Alhamis ya sabunta adadin mutanen da suka mutu sakamakon arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro a fadin kasar zuwa kusan 50, inda ya sanar da kafa dokar hana fita.

Mutuwar dai ta fi faruwa ne a babban birnin kasar N’Djamena da kuma biranen Moundou da Koumra, inda ya kara da cewa dokar hana fita za ta ci gaba da kasancewa har sai an maido da kwanciyar hankali a wuraren da tashe-tashen hankula ke faruwa.