Ambaliyar ruwa ta mamaye gidan tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan

0
76

Ambaliyar ruwa ta mamaye gidan tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan da ke mahaifarsa, Otuoke a Hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa.

A ziyarar jaje da ya kai Utuoke, a ranar Juma’a, Gwamna Duoye Diri, ya bayyana damuwa bisa yawan barnar da ambaliyar ta yi wa al’ummar garin, wanda ya kira, “ibtila’in da ya shafi rayuwar al’ummar Bayelsa.”

Ya ce, “Ruwa ya mamaye gidan tsohon shugaban kasa, ya mayar da shi dan gudun hijira. A garin kuma a kwai Jami’ar Tarayya.

“Jama’ar Ogbia na zo da kaina ne domin gabin halin da Otuoke ke ciki da kuma ba ku kwarin gwiwa. Sannan ku sani cewa ba ku kadai irin wannan ibtila’i ya shafa a fadin jihar nan ba,” inji Gwaman Diri.

Kusan daukacin garin da ke mazaunin Jami’ar Tarayya, ruwa ya shanye shi, kuma yawancin mutanen garin na gudun hijira, cikinsu har da tsohon shugaban kasa Jonathan.

Gwamnan ya roki mutanen da kada su yanke kauna, yana mai ba su tabbacin samun tallafin abin ci da magunguna da sauran bukatu daga gwamnatin jihar.