Gwamnati ta kwaso ’yan Najeriya 542 da suka makale a Dubai

0
41

Gwamnatin Najeriya ta kwashe ’yan kasar kimanin 542 da suka makale a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Hukumar Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Ketare, NIDCOM ce  ta bayyana hakan cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Tuwita.

NIDOCM ta ce da misalin karfe 4:29 na asubahin ranar Lahadi ne jirgin da ya kwaso mutanen ya sauka a filin jirgin saman Abuja, babban birnin kasar.

NIDCOM ta ce cikin wadanda aka kwaso akwai mata 460, maza 79 da kuma kananan yara uku.

Haka kuma, ta ce gwamnatin ta bai wa kowannensu dala dari-dari domin su yi jigilar komawa gidajensu daga filin jirgin saman na Nnamdi Azikiwe.

Wannan na zuwa ne ’yan kwanaki bayan da Hukumar Shige da Fice ta kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta bayyana dakatar da bai wa ’yan Najeriya biza, saboda wasu matsaloli da suka shafi diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Rahotonni sun ambato gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa na cewa duka wadanda suka cika takardun neman biza za a mayar musu da takardunsu ba tare da samun amincewa ba.

Ta kuma ce “kin amincewar ya shafi kowanne dan Najeriya, don haka babu wanda za a ba shi biza a halin yanzu.”

A baya-bayan nan dai dangantaka na kara yin tsami tsakanin kasashen biyu, inda a watan da ya gabata kasar ta UAE ta daina bayar da bizar yawon bude ido ga ’yan kasa da shekara 40, lamarin da ya shafi ’yan Najeriya da na wasu kasashen.

Haka kuma a shekarar 2021 ma kasashen biyu sun shafe watanni masu yawa suna ce-ce-ku-ce game da harkar sufurin jiragen sama.