Kwankwaso zai bayyana manufofin takararsa a ranar 1 ga watan nuwamba

0
56

A ranar 1 ga watan Nuwamba ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso zai bayyana manufofin takararsa na shugaban kasa.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Dage bikin kaddamar da manufofin takarar shugaban kasa na dakta Rabiu Musa Kwankwaso,’ wanda jam’iyyar NNPP ta fitar ranar Talata.

Jam’iyyar ta kuma sanar da dage taron, inda ta ce a yanzu za a gudanar da taron ne a ranar 31 ga watan Oktoba.

Jam’iyyar ta ce ta dage taron ne biyo bayan kiranye-kiranye da ‘ya’yan jam’iyyar da kuma masu ruwa da tsakin jam’iyyar suka yi.

A wani bangare sanarwar ta kara da cewa, “Karo na 3 na taron RMK, wanda wani bangare ne na gudanar da bikin cikar Mai Girma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso shekaru 66 da haihuwa, yanzu zai gudana ne a ranar Litinin 31 ga Oktoba 2022 da misalin karfe 10:00 na safe a dakin taro na A. -Class Park and Events Center, da ke Wuse II, a Abuja.

“A wannan rana, Sanata Kwankwaso zai gana da shuwagabannin jihohi, da ‘yan takarar sanata da sauran masu ruwa da tsaki domin yin nazari tare da duba tsarin manufofinsa ga Nijeriya da ‘yan Nijeriya, yayin  kaddamar da manufofin a ranar Talata 1 ga watan Nuwamba. 2022.

“Yayin da muke nadamar duk wata matsala da dage taron da aka yi zai haifar ga ‘ya’yan jam’iyyarmu masu daraja, muna kira ga ‘yan uwa na jam’iyyar NNPP da su rubanya kokarinsu wajen ganin sun samu gagarumar nasara ga jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.