‘Yan fasakauri sun harbe jami’in kwastam a jihar Kwara

0
73

Wasu da ake zargin ’yan fasa kauri ne sun kashe wani jami’in kwastam mai suna Saheed Aweda, wanda ke aiki a sashin kula da kan iyaka (JBPT) a shiyya ta 3 a jihar Kwara.

‘Yan fasa kwarin, wadanda rahotanni suka nuna cewa, sun yi wa jami’an Kwastam kwanton bauna ne a kan hanyar Sinau-Kenu a karamar hukumar Baruten ta jihar, garin da ke kan iyaka, sun kuma raunata wasu daga cikin jami’an tawagar JBPT guda uku.

An yi jana’izar jami’in kwastam din da aka kashe kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a gidansa da ke Ilorin.

Kakakin hukumar kwastan na jihar Kwara, Chado Zakari, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya tabbatar da cewa wanda aka kashe da jami’an uku da suka samu rauni, sun sami bayanan sirri ne kan wani fasa kwari kafin ‘yan bindigar su far musu a ranar Juma’a.

Zakari ya ce, Jami’an sun kama buhu 40 na shinkafa ‘yan kasar waje da kuma jarkoki 30 na man fetur (PMS) kowacce dauke da lita 25, wanda ‘yan fasa kaurin suka zubar acikin daji, kan titin hanyar Sinau-Kenu.